A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, cikakken saƙon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ga shi kamar haka:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
Ranar 22 ga watan Bahman a kowace shekara, ita ce ranar bayyana ƙarfi da darajar al’ummar Iran. Al’ummar da godiya ta tabbata ga Allah, suna da karsashi, da nufi, da juriya, da kuma sanin abin da yake da amfani ko cutarwa a gare su. A ranar 22 ga Bahman na farko da aka yi nasara, al’ummar Iran sun samu babban rabo; sun sami damar ceto kansu da ƙasarsu daga tsoma bakin baƙi. Waɗannan baƙi a tsawon waɗannan shekaru koyaushe suna son mayar da tsohon yanayin (mulkin kama-karya).
Al’ummar Iran sun tsaya tsayin daka. Alamar wannan juriya ita ce ranar 22 ga Bahman. Wannan tattaki na nuna goyon baya da babu irinsa a duniya. Ba mu taɓa samun labarin wata ƙasa a duniya ba, inda bayan shekaru masu yawa, ake gudanar da ranar samun 'yancin kai da ranar ƙasa da irin wannan gagarumin taron jama’a a duk faɗin ƙasar don nuna kansu. A yau, al’ummar Iran suna nuna kansu ta hanyar fitowa kan tituna, kuma wannan yana tilasta wa waɗanda suke da ƙuƙuntar zuciya akan Iran ta Musulunci da Jamhuriyar Musulunci su ja da baya.
Ikon ƙasa ya fi danganta da nufin al’ummu da juriyarsu fiye da yadda yake danganta da makamai masu linzami (missiles) ko jiragen sama. Godiya ta tabbata ga Allah, kun nuna juriya kuma kun nuna nufinku. Ku sake nuna hakan a cikin lamura daban-daban. Ku sanya maƙiyi ya yanke ƙauna. Muddin maƙiyi bai yanke ƙauna ba, al’umma za su ci gaba da fuskantar tsangwama. Dole ne a sanya maƙiyi ya yanke ƙauna.
Yanke ƙaunar maƙiyi yana samuwa ne ta hanyar haɗin kanku, da ƙarfin tunani da nufinku, da karsashinku, da kuma juriya a gaban waswasin maƙiya. Waɗannan su ne suke gina ikon ƙasa. Insha Allahu matasanmu a fage daban-daban, a fagen ilimi, a fagen aiki, a fagen taƙawa da ɗabi’u, da kuma fagen ci gaban duniya da na lahira, za su ci gaba da samun nasara don samar da alfahari ga ƙasa. Ranar 22 ga Bahman ita ce bayyanar duk waɗannan abubuwa. Kowa yana fitowa kan tituna yana rera taken goyon baya, suna bayyana gaskiya da kuma nuna haɗin kansu; al’ummar Iran suna bayyana biyayyarsu ga Jamhuriyar Musulunci.
Muna fatan insha Allahu wannan 22 ga watan Bahman, kamar sauran shekarun da suka gabata, zai ninka ɗaukaka da kwarjinin al’ummar Iran, sannan ya tilasta wa sauran al’ummu, gwamnatoci, da manyan ƙasashe miƙa wuya da girmama al’ummar Iran, wanda insha Allahu hakan ne zai kasance.
Wassalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh
20/11/1404
09/02/2026
Your Comment